Connect with us

Business

Kuɗin Ghana, cedi shine mafi ƙarancin daraja a kan Dalar Amurka a duniya

Published

on

Takardar kudin na cedi

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Kudin cedi na Ghana ya zama mafi karancin daraja a kan Dalar Amurka a duniya bayan da ya faɗi da kashi 45.1 na darajar sa ga dalar Amurka a bana.

Advertisement

A cewar Bloomberg, kudin ƙasar wacce ita ce ta biyu a noman cocoa a duniya, ya ragu da kashi 3.3 a jiya Litinin zuwa 11.2750 kowace dala.

 

Advertisement

Matawalle Ya Nemi Afuwar Kafofin Yada Labaran Da Ya Rufe

Kamfanin yada labaran ya ce ƙarancin darajar ta cedi a kan dala shi ne mafi muni a cikin kudade 148 da aka gano.

Advertisement

Hakan ya sa yanzu cedi ya yi ƙasa da rupee na Sri Lanka, wanda yanzu shine mafi muni na biyu tare da raguwar kashi 44.7 cikin dari zuwa Dalar Amurka a wannan shekara.

A cikin watan Yuli, Ghana ta fara shiga tsakani da Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) don wani shirin ceto don maido da kwanciyar hankali a fannin tattalin arziki.

Advertisement

Tabarbarewar tattalin arziki da hauhawar farashin kayayyaki a kasar da ke yammacin Afirka ya tilasta wa daruruwan ‘yan kasar fitowa kan tituna domin nuna adawa da karin farashin, haraji kan biyan kudin lantarki, da sauran haraji.

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Daily Nigeria Hausa

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending