Connect with us

News

Matuƙa jiragen saman Kenya za su shiga yajin aiki

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Bayanai sun tabbatar da cewa yajin aikin matuƙa jiragen saman zai fara ne daga tsakiyar daren nan, abin da zai haifar da soke tashin jiragen saman Kenya Airways, musamman daga filin jirgin sama na Nairobi, babban birnin ƙasar.

Advertisement

 

Buƙatar matuƙa jiragen saman ita ce kamfanin ya ci gaba da bayar da tasa gudumawar a asusun tara kuɗaɗen fanshon ma’aikata, wanda ya tsayar a lokacin annobar korona.

Advertisement

Masu ruwa da tsakin APC na karamar hukumar Doguwa sun ziyarci Sulen Garo

A nasa ɓangaren, kamfanin ya ce yana cikin matsalar kuɗi kuma ba zai iya ci gaba da biyan kuɗaɗen ba har sai tsakiyar shekarar 2023.

Advertisement

 

Kamfanin jiragen saman na Kenyan Airlines ya rinƙa tafka hasara a kusan shekara biyar da suka gabata, inda sau da dama yake dogaro da tallafin kuɗin da yake samu daga gwamnati.

Advertisement

 

Kuma kamfanin ya ce zai yi hasarar kuɗi dala miliyan 2.5 a kowace rana idan matuƙa jiragen suka shiga yajin aiki.

Advertisement

 

Mako biyu da suka gabata ne ƙungiyar ma’aikatan ta bayar da sanarwar aniyarta ta shiga yajin aikin.

Advertisement

 

Ɓangarorin biyu sun rinƙa nuna wa juna yatsa, inda ƙungiyar matuƙa jiragen ta zargi shugabannin kamfanin jiragen da laifin tsangwamar ma’aikatan da ke hanƙoron ganin sun bi ‘haƙƙoƙinsu.’

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending