Connect with us

News

Yan Bindiga Sun Yi Wa Hakimi Yankan Rago A Kebbi.

Published

on

Yan bindiga

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

Akalla mutum hudu ne aka kashe, ciki har da wani hakimi da aka yi wa yankan rago, yayin da wasu ‘yan bindiga suka kai garin Tunga Rafin da ke Karamar Hukumar Augie a Jihar Kebbi a daren Laraba.

Advertisement

 

Liberty rawaito ‘yan bindigar da yawansu ya haura 70 ne suka kai farmaki kauyen cikin dare, inda suka kashe Hakimin yankin mai suna Abubakar Magaji (Sabo Rafi) da wani mutum guda.

Advertisement

Mun Lalata Haramtattun Matatun Mai Sama Da 70 Cikin Mako 2 – Sojoji

 

Advertisement

Wani mazaunin kauyen da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce maharan sun kuma yi awon gaba da mata da yaron Hakimin bayan sun yi masa yankan rago.

 

Advertisement

Ya ce ‘yan bindigar sun kuma kashe wasu mutum biyu da suka ci karo da su a hanya yayin da suke ficewa daga kauyen.

 

Advertisement

“Sun gudu lokacin da suka fahimci mutanenmu suna kokarin kai musu hari,” inji shi.

 

Advertisement

Ya ce wannan ne karon farko da ‘yan bindiga suka kai hari kauyen duk da cewar suna farmakar makwabtansu.

 

Advertisement

“Ba mu san za su kai mana hari nan kusa ba, duk da cewa sun sha kai hari ga wasu yankunan.

 

Advertisement

“Mutane da yawa sun fito domin dakile harin da suka kai wa al’umma amma sai suka kashe shugaban kauyenmu da wasu mutum uku sannan suka gudu,” in ji shi.

 

Advertisement

Da aka tuntubi Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar, SP Nafiu Abubakar, ya ce har yanzu ba su tabbatar da faruwar lamarin ba.

 

Advertisement

Sai dai ya yi alkawarin yin karin haske da zarar ya samu wani bayani.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending