News
‘Bam’ Ya Kashe Mutum 2 A Kaduna
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Wasu mutum biyu sun mutu yayin da wani abu da aka binne ya fashe ya kuma tashi da su a Karamar Hukumar Chikun ta jihar Kaduna.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 2:00 na yammacin Alhamis.
Mun Lalata Haramtattun Matatun Mai Sama Da 70 Cikin Mako 2 – Sojoji
Motar wadanda abin ya rutsa da su ta bi ta kan abin fashewar da ake zargin ’yan ta’adda ne suka dasa a Zangon Tofa a yankin Kabrasha.
Aminiya ta rawaito cewa mutanen kauyen na jigilar amfanin gonar da suka girbe lokacin da lamarin ya afku.
Kwamishinan Tsaro da Al’amuran Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin, ya ayyana mutum biyu a matsayin wadanda suka rasa rayukansu; Babajo Alhaji Tanimu da Safiyanu Ibrahim.
A cewarsa, Gwamnatin Jihar na bincike kan lamarin.
Ya kuma ce Gwamnan Jihar, Nasiru El-Rufai, ya jajanta wa iyalan wadanda abin ya shafa.
-
News5 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News3 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News5 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
