Connect with us

News

2023: Kotu Ta Hana ‘Yan Takarar Majalisar APC 16 Yin Takara A Ribas 

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a garin Fatakwal na jihar Ribas, a ranar Juma’a, ta kori ‘yan takara 16 da ke neman kujerun majalisar dokokin jihar a karkashin jam’iyyar APC, daga tsayawa takara a zaben 2023.

 

Advertisement

Jihar Ribas tana da mazabu 32 inda yankin Ribas ta Gabas ke da rinjaye.

 

Advertisement

 

Jam’iyyar PDP ta maka Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da wasu mutane 33 a kotu, inda ta nemi a haramta wa ‘yan takarar jam’iyyar APC takara bisa zargin hukumar zaben ba ta sanya ido a zaben jam’iyyarsu ba.

Advertisement

 

Darajar Naira ta fara farfaɗowa a kasuwa  -Za ta ɗore ko kuwa?

Advertisement

Da yake yanke hukunci a kan kara mai lamba: FHC/PH/CS/152/2022, alkalin kotun, mai shari’a Mohammed Turaki Adamu, ya yanke hukunci a kan wadanda suka shigar da kara.

 

Advertisement

Wadanda abin ya shafa sun hada da Andoni, Etche I da II, Tai, Gokana, Oyigbo, Eleme, da Fatakwal I, II da III, Khana I da II Okrika, Ahoada West da Obio/Akpor I da mazabar II.

 

Advertisement

 

Leadership hausa ta rawaito cewa A halin da ake ciki, shugabancin jam’iyyar APC a jihar ta yi kira ga mambobinta da magoya bayanta da kada su yi kasa a gwiwa da hukuncin da babbar kotun tarayyar ta yanke.

Advertisement

 

Majalisar zartarwa jam’iyyar APC, a wata sanarwa da ta fitar a Fatakwal a ranar Juma’a ta hannun mai magana da yawun jam’iyyar, Sogbeye Eli, ta tabbatar da cewa jam’iyyar na yin wani yunkuri na daukaka kara kan hukuncin da kotun ta yanke.

Advertisement

 

Sanarwar ta ci gaba da cewa: “A halin da ake ciki, Majalisar zartarwa tana kira ga mambobin jam’iyyar da miliyoyin al’ummar Ribas da ke goyon bayan ‘yan takararmu a mazabar da abin ya shafa da kada su yanke kauna ko kuma su tayar da hankali yayin da muke shirin daukaka kara don sauya hukuncin kotun dom dawo da ‘yan takararmu kafin zabe.

Advertisement

 

“Idan za a tuna cewa INEC ita ce ta jagoranci tabbatar da cewa ta sanya ido a kan zaben fidda gwanin APC a gaban wani Alkalin Babbar Kotun Tarayya da ke Fatakwal a wani batu da ke kalubalantar cancantar ‘yan takararmu na Majalisar Tarayya.

Advertisement

 

“Makiyan dimokuradiyya a jiharmu da suke tsoron haduwa da mu a zabe, sun fito ne don karya lagonmu, do tilasta wa ’yan takararmu amma sun kasa.

Advertisement

 

“Za mu yi takara a zabukan da ke tafe a dukkan matakai kuma za mu yi nasara bayan ajiye wannan hukunci a gefe kamar yadda kundin tsarin mulki ya bai wa jam’iyyar APC dama.”

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending