News
Ɗalibin BUK ya zama shugaban ƙungiyar LAWSAN ta Najeriya
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kwamared Yasir Abubakar, ɗalibi mai karantar Shari’a a jami’ar Bayero da ke Kano, kuma ɗan aji 4, ya zama shugaban ƙungiyar ɗalibai lauyoyi ta Najeriya, mai suna LAWSAN.
Hukumar zaben ƙungiyar ta tabbatar da lashe zaɓen da Yasir ya yi bayan ya samu ƙuri’u 30 a zaɓen da aka gudanar a otal ɗin Swiss Spirit Hotel, da ke garin Fatakwal a Juma’ar da ta gabata.
Abubakar dai ya kayar da abokin karawarsa Ann Lyam Iverem daga jami’ar Bingham a jihar Nasarawa, wanda ya sami ƙuri’u 26.
Bayan gudanar da zaɓen, wasu daga cikin mahalarta zaɓen sun nuna murnarsu gami da tabbacin cewa lallai Yasir zai taɓuka abin kirki da yardar Allah.
#TDRHausa
-
News1 day ago
Jam’iyyar Labour Party Ta Yi Alkawarin Kafa Hukumar Kula Da Hayar Gidaje A Kano
-
News3 days ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News6 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
