Sports
Sarki Salman na Saudiyya ya bayar da hutu bayan ƙasar ta doke Argentina
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Advertisements
Advertisements
Sarki Salman bin Abdul Aziz na Saudiyya ya ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu a faɗin ƙasar.
Ya bayar da hutun ne domin ‘yan ƙasar kama daga ma’aikatan gwamnati da masu zaman kansu da ɗalibai a dukkan matakan ilimi daban-daban na ƙasar, su samu damar yin murnar nasarar da ƙasar ta samu kan Argentina a gasar ƙwallaon ƙafa na diuniya da ke gudana a ƙasar Qatar.
A ranar Talata da rana ne ƙasar ta Saudiyya ta samu nasarar doke Argentina da ci 2-1 a wasan farko na cikin rukuni da suka fafata a filin wasa na Lusail.
Advertisements
