Connect with us

News

Yan sanda 2 sun mutu, 17 sun jikkata a wani haɗarin mota a hanyar Borno

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta tabbatar da mutuwar ƴan sanda biyu a wani haɗarin mota inda wasu 17 suka jikkata.

Advertisement

 

Haɗarin ya afku ne a jiya Litinin a kan hanyar Hawan Kibo a jihar Plateau yayin da ƴan sandan ke kan hanyar Uyo domin gudanar da wasannin ƴan sanda na 2022.

Advertisement

Qatar 2022: Barcelona Ta Kafa Tarihi A Gasar Cin Kofin Duniya

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, Sani Shatambaya, ya fitar a yau Talata a Maiduguri.

 

Advertisement

Ya ce tawagar za ta wakilci shiyya ta 15 da ta kunshi Borno da Yobe a gasar ‘yan sanda a Uyo, Akwa Ibom.

 

Advertisement

Kakakin ya ce hatsarin ya afku ne sakamakon shanyewar birki, inda ya kara da cewa wadanda suka mutu ‘yan sanda ne mata.

 

Advertisement

A cewar Shatambaya, an yi jana’izar da ta dace da wadanda suka mutu yayin da wadanda suka jikkata ke karbar kulawa a asibitoci daban-daban a Maiduguri.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending