Connect with us

News

Aisha Buhari: Kotu ta tura Aminu Muhammad gidan yari

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

BBC ta gano cewa an gabatar da Aminu Muhammad da ake zargi da cin mutuncin matar Shugaban Najeriya, Aisha Buhari gaban kotu jiya Talata, kuma tuni ma an garzaya da shi gidan yari.

 

Advertisement

Lauyan dalibin CK Agu ya tabbatar wa da BBC cewa an gurfanar da wanda yake karewar a gaban wata kotu da ke Abuja babban birnin kasar, kuma bai amsa laifin da ake zargin shi da aikatawa ba.

Kuto ta aika da shugaban jam,iyyar APC gidan yari

Mr Agu ya ce tun ranar 25 ga watan Nuwamba suka nemi a bada Aminu beli amma hakan ba ta samu ba.

Advertisement

 

”Ko a zaman kotun na jiya mun sanar da alkali cewa mun bukaci yan sanda su ba da Aminu beli cikin lokaci amma ba su amsa mana cewa za su sake shi ba ko a akasin haka.”

Advertisement

 

”Akan haka muka bukaci kotun ta bada shi beli bisa dalilan rashin lafiya da kuma cewa zai fara jarabawa a makaranta ranar 5 ga watan Disamba. Kuma a yanzu kotun ta umurci rundunar yan sanda ta gabatar da bukatar belin da aka shigar da gaggawa don kotu ta samu damar sauraren bukatar yau ko gobe,” in ji CK Agu.

Advertisement

 

Tun da farko iyayen dalibi Aminu Muhammad sun fada wa BBC cewa za a gurfanar da dan nasu kotu yau Laraba, kafin daga baya lauyansa ya tabbatar da cewa an fara zaman jiya Talata, kuma za a sake wani zaman yau ko gobe don duba bukatar ba da shi beli.

Advertisement

 

Da aka tambayi lauyan inda Aminu yake a halin yanzu sai yace ” yanzu haka yana tsare a gidan yarin Suleja kafin a saurari bukatar bada shi beli.”

Advertisement

 

Tsare Aminu Muhammad wanda dalibi ne a jami’ar tarayya da ke Dutse a jihar Jigawa ya tayar da kura musamman a shafukan sada zumunta, inda da dama ke zargin kama shi da tsare shi ba bisa ka’ida ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending