Sports
Netherlands ta tsallaka mataki na gaba bayan doke Amurka da ci 3-1 a Qatar
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Netherlands ta dawo cikin kungiyoyin kwallon kafa da suka sake samun rubu’in gasar cin kofin duniya bayan doke Amurka da ci 3-1 a yau Asabar a Qatar, inda za su kalubalanci ko dai Argentina na Lionel Messi, ko Australia.
A filin wasa na Khalifa International Stadium, kwallaye uku daga Memphis Depay da Daley Blind da Denzel Dumfries suka zura a ragar Amurka, yanzu dai Netherlands za ta iya numfasawa yan kwanaki kafin wasan daf da na kusa da na karshe, wanda za a yi ranar Juma’a mako mai kamawa a filin wasa na Lusail, yayin da suke jiran sanin ko wane ne abokin karawarsu.
Zai iya zama Argentina don sake fafatawa a wasan kusa da na karshe kamar dai yada ta gudana a 2014 a bugun fenariti da Messi da sauransu suka yi kafin faduwa a wasan karshe.
