Sports
Qatar 2022: Yau za a shiga zagayen gaba a gasar Kofin Duniya
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Bayan da aka kammala wasannin cikin rukuni a jiya, a yau kuma za a shiga matakin sili-ɗaya-ƙwale a gasar cin Kofin Duniya da ke gudana a ƙasar Qatar.
Ƙasashe 16 ne suka samu nasarar tsallakawa wannan mataki bayan da kowacce ƙasa ta yi fafatawa uku-uku a cikin rukuni.
Kawo yanzu dai ƙasashen Afirka biyu ne suka rage a cikin gasar da suka haɗar da Morocco wadda ta ja ragamar rukuni da shida, sai kuma Senegal da ta zo ta biyu a rukuni na ɗaya.
A yau za a fara karawar matakin ‘yan 16 da suka rage a gasar tsakanin Netherlands da Amurka sai kuma gumurzu tsakin Argentina da Australiya
Advertisements
