Connect with us

Sports

Ko kun san nawa duk tawagar da ke gasar kofin duniya ta Qatar za ta samu?

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

 

 

A bana, hukumar kula da kwallon kafa ta duniya FIFA ta kara yawan kudin kyautar da ake bai wa kasashen da suka samu gurbin buga gasar lashe kofin duniya da ke gudana a kasar Qatar, da dala miliyan 40 maimakon dala miliyan dari 400 da ake kashewa.

 

Advertisement

 

Tun a watan Afrilun wannan shekarar ne dai hukumar ta FIFA ta sanar da bai wa kasashen da suka samu gurbin buga gasar dala miliyan daya da rabi don shirya wa gasar.

Wata kungiyar Saudiyya ta yi wa Ronaldo tayin kwantiragin Fam miliyan 300

Haka nan kowace tawagar kasar da ta halarci gasar ta bana cikin 32 sai da aka ba su dala miliyan 9 a matsalin kudin rukuni.

 

Duk wata kasa da ta samu damar tsallakawa zuwa zagaye na biyu na kasar, za ta samu dala miliyan 13, inda a jimillance kasashe 16 za su raba dala miliyan dari da hudu.

 

Advertisement

Sai matakin zagayen dab da na kusa dana karshe wato quarter-finals, inda kasashe 8 da suka kai wannan mataki za su samu dala miliyan 68, inda kowaccen su za ta samu dala miliyan 17.

 

Hakuma fri hausa ta rawaito cewa Kasar da ta kare a mataki na hudu za ta samu dala miliyan 25, sai kuma wacce ta kare a mataki na uku za ta samu dala miliyan 27.

 

Haka nan hukumar FIFA ta ware kyautar dala miliyan 30 ga duk kasar da ta kare a mataki na 2.

 

Advertisement

Duk kasar da ta samu nasarar lashe gasar ta bana kuwa zata samu zunzurutun kudi har dala miliyan 42.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending