Sports
Wata kungiyar Saudiyya ta yi wa Ronaldo tayin kwantiragin Fam miliyan 300
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Cristiano Ronaldo ya samu tayi mai tsoka daga Saudi Arabia bayan da ya rabu da Manchester United sai dai dan wasan gaban ya kudiri aniyar sai ya kammla gasar kofin duniya Qatar kaafin ya yi Magana a kan makomarsa.
Kungiyar kwallon kafa ta Al-Nassr ce ta nuna tana son Ronaldo, inda ta ce za ta ba shi fam miliyan 100 a duk shekara har na tsawon shekara 3 da rabi.
Wasu majiyoyi sun ce Al-Nassr ta ce a shirye take ta biya Ronaldo hakkokinsa da ya kamata ya samu idan da ya kammala kwantiraginsa da ya rage a United, wanda ya kai fam miliyan 16.
Ronaldo mai shekaru 37, ya bukaci wakilansa su dakatar da duk wata tattaunawa a game da makomarsa a yayin da yake a Qatar, amma majiyoyi sun tabbatar da cewa an fara tattaunawa kan komawarsa Al-Nassr.
Kyaftin din tawagar Portugal din ya rabu da Manchester United ne ba tare da an biya shi kudin sallama ba, biyo bayan tattaunawar fahimtar juna da suka yi, sakamakon caccakar kocin kungiyar da wasu manyan jami’ai a wata hirar talabij
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days agoWakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
