Connect with us

News

Kano: Sha’aban Ya Gana Da Malamai, Ya Yi Alkawarin Kafa Cibiyar Nazarin Al-kur’ani. 

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Dan Majalisar Wakilai Honarabul Sha’aban Ibrahim Sharada ya gabatar da kudirin kafa cibiyar binciken al-Qur’ani ta kasa a Kano wanda ya ke Wakiltar Karamar Hukumar Birni, kuma Dan Takarar Gwamnan jihar Kano a jam’iyyar ADP a zaben 2023.

Advertisement

 

Sharada ya bayyana hakan ne a lokacin da ya sanar da malaman Kano shawararsa ta tsayawa takarar gwamnan jihar.

Advertisement

 

An umurci mutane su zauna cikin shirin ko-ta-kwana bayan aman dusten Lascar

Jaridar indaranka ta rawaito cewa Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Abbas Yushau Yusuf, kakakin majalisar yakin neman zaben gwamnan jihar na ADP ya fitar a ranar Lahadin nan.

Advertisement

 

 

Advertisement

 

A cewar Sharada, za a gudanar da karatun farko da na biyu don samar da cibiyar a cikin makonni masu zuwa.

Advertisement

 

Sharada ya sanar da Malamai cewa cibiyar binciken kur’ani, inda ake sa ran za ta kasance a Kano ganin yadda Kano ta yi galaba a wajen masu haddar al-Qur’ani a Najeriya.

Advertisement

 

Jaridar Indaranka ta rawaito cewa shi dan majalisa kuma dan takarar gwamnan ADP ya bayyana cewa idan aka zabe shi gwamna zai wajabta karatun Al-Qur’ani a Kano a makarantun firamare da na gaba tunda yana da sha’awar bunkasa fannin ilimi.

Advertisement

 

 

Advertisement

Dan takarar ya bayyana cewa yana ganin yana da matukar muhimmanci ya gana da su tare da bayyana musu muradinsa na tsayawa takarar gwamnan jihar Kano tun da malamai na da matukar muhimmanci da kuma masu ruwa da tsaki wajen tafiyar da tunanin dan kasa.

 

Advertisement

Ya kara da cewa, lokaci ya yi da gwamna ya kamata ya zama jagora ga talakawansa sannan kuma malamai su zama mataimaka wajen aiwatar da manufofi da tsare-tsare na gwamnati.

 

Advertisement

Ya kuma yi godiya ga malaman da suka amsa gayyatar da aka yi musu, ya kuma ce zai ci gaba da ganawa da su kan muhimman batutuwa a matsayinsu na shugabannin al’umma.

 

Advertisement

Dan takarar ya kawo ayoyin kur’ani mai tsarki da ke nuna muhimmancin tuntubar juna da shigar da malamai cikin al’amuran jama’a.

 

Advertisement

 

Daga cikin fitattun malaman addinin musulunci da suka halarci wannan taro akwai babban limamin masallacin Alfurqan Dr Bashir Aliyu Umar da Sheikh Abdulgaffar Nasiru Kabara da Sheikh Lawal Abubakar Triumph da Dr Abdullahi Muhammad Getso da Sheikh Tijjani Zangon BareBari da sauran su da dama daga dukkan darikun jihar Kano.

Advertisement

 

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending