Connect with us

News

Mutum shida sun mutu a haɗarin mota a Kogi

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Hukumar kiyaye haɗura ta jihar Kogi, ta tabbatar da mutuwar mutum shida yayin da wasu 25 suka samu raunuka a haɗarin mota kan hanyar Okene-Ogori da ke jihar Kogi yau Asabar.

 

Advertisement

Babban kwamandan hukumar, mista Stephen Dawulung, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN a Lokoja cewa haɗarin ya faru ne lokacin da wata mota dauke da mutane 45 da kuma wasu shanu.

An kama mai shekara 75 da zargin yi wa mai shekara huɗu fyaɗe a Jihar Nasarawa

Kwamandan ya ce haɗarin wanda ya faru da misalin 12 na rana, ya yi sanadiyar mutuwar wasu daga cikin shanun.

Advertisement

 

Ya kara da cewa bayan faruwar lamarin, ya aike da jami’ansa zuwa wurin, inda a halinn aka tafi da wadanda suka samu raunuka zuwa asibiti domin yi musu magani yayin da aka girke gawarwakin wadanda suka rasu a mutuware da ke garin na Okene.

Advertisement

 

Babban kwamandan ya yi kira ga direbobi da su kasance masu bin dokokin hanya a kodayaushe domin afkuwar haɗari da tsira da rayukansu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending