Connect with us

Sports

Benzema ya sanar da kawo karshen bugawa Faransa wasa

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

 

 

Karim Benzema ya sanar da yin ritaya daga buga kwallon kafa a kasa da sa’o’i 24 bayan da Faransa ta sha kashi a hannun Argentina a wasan karshe na cin kofin duniya na 2022.

 

Benzema yana cikin tawagar Faransa domin buga wasa a Qatar amma ya samu rauni a cinyarsa wanda hakan ya sa ba zai bugawa  kasar ba.

Advertisement

Hatsarin Mota: Mutum 11 Sun Kone Kurmus A Hanyar Zariya Zuwa Kano

 

Da yake sanar da hukuncin ranar cikarsa shekaru 35 da haihuwa. ya rubuta, “Na yi ƙoƙari da kurakuran da aka yi don zama inda nake a yau kuma ina alfahari da shi! Na rubuta labarina kuma namu yana ƙarewa”.

 

Benzema ya fara buga wasansa na farko a duniya a 2007 a Les Bleus inda ya zura kwallaye 37 a wasanni 97.

 

Dan wasan mai shekaru 35 ya kasance ba a cikin hoton tawagar kasar tsawon shekaru biyar bayan da aka same shi da hannu a wani laifin da ya shafi kaset din jima’i da ya girgiza kwallon Faransa.

Advertisement

 

Kocin Faransa Didier Deschamps ya tuno da shi a shekarar 2021 gabanin gasar cin kofin nahiyar Turai, inda ya zura kwallaye hudu a wasan da aka yi a zagaye na 16.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending