Connect with us

News

Yadda mata mafarauta suka shiga yaki da ‘yan bindiga a Taraba

Published

on

DAGA MARYAM BASHIR MUSA 

 

Advertisement

 

A jihar Taraba da ke arewa maso gabashin Najeriya, mata mafarauta ne suka bi sahun takwarorinsu maza wajen yaki da ‘yan bindiga a jihar.

Advertisement

 

Jaridar Daily Trust, ta rawaito cewa matan sun hadar da masu aure da kuma marasa aure.

Advertisement

Okupe ya biya tarar naira miliyan 13 don gujewa zaman gidan yari

Matan sun ce sun shiga a dama da su a yakin ne saboda su taimaka wa mazan wajen murkushe ‘yan bindigar da suka addabi jihar.

 

Advertisement

Matan sun ce, ana kashe mutane maza da mata har da yara a wasu sassan jihar, yayin da ake sace wasu ciki har da matan aure da yammata sannan ayi musu fyade musamman a yankunan Karim-Lamido, da Gassol da kuma karamar hukumar Bali.

 

Advertisement

Matan sun ce irin wadannan abubuwa da ke faruwa ne ya sa su shiga cikin kungiyar mafarautan da ke yaki da ‘yan bindiga a jihar.

 

Advertisement

Sun ce suna da kwarin gwiwa kuma ba sa tsoro don haka a shirye suke su shiga cikin yakin da ake da ‘yan bindiga a jihar ta Taraba don murkushe su.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending