News
Najeriya Za Ta Cefanar Da Wasu Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarki
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Gwamnatin Najeriya ta ce a rubu’in farko na shekarar 2023, za ta saida kamfanonin wutar lantarki biyar domin cike gibin kasafin kudin badi.
Wannan na zuwa ne watanni shida bayan gwamnati ta sanar da shirin gyaran kamfanonin da ke rarraba wutar lantarki kasar nan.
Jaridar Premium Times ta rawaito cewa kasafin kudin badi da Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar a watan Oktoba da ya gabata, sun kai sama da naira tiriliyan 20, ya yin da ake fargabatar ta yiwu sai an ciwo bashin da za a cike gibin kasafin kudin kasancewa kudaden shiga da gwamnatin Najeriyar ke samu sun dan ja da baya.
Kamfanonin da cefanen zai shafa sun hada da Geregu power plant, da ke samar da megawat 562 da ke Calabar, da wani a jihar Cross River, sai kuma na dayan da ke Olorunsogo.
A bangare guda kuma, matakin cefanar da kamfanon lantarkin na zuwa ne a daidai lokacin da wutar ba ta wadaci ‘yan kasar ba, da kuma karin kudin da aka yi.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
