News
Yan Majalisar Wakilan Najeriya na shirin yaƙi da dokar cire kuɗi ta CBN
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Wasu ‘yan Majalisar Wakilan Najeriya sun ci alwashin tilasata wa Babban Bankin ƙasar (CBN) wajen dakatar da shirinsa na rage yawan adadin kudin da ‘yan ƙasa da kamfanoni kan cira a kullum, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Karamin soja Mai mukamin kofur yayi yunkurin juyin Mulki
Wani daga cikin shugabanni a Majalisar ya faɗa wa jaridar cewa akasarinsu sun aminta cewa ya kamata a jingine dokar baki ɗayanta.
A cikin sabuwar dokar, mafi yawan abin da mutum zai iya cirewa a mako na tsabar kuɗi shi ne naira N100,000, kamfani kuma N500,000. Daga baya aka ƙara ya zama N500,000 ga mutane da kuma 5,000,000.
Tun da farko Majalisar ta nemi CBN ya jinkirta fara amfani da dokar tukunna, wadda za ta fara aiki daga 9 ga watan Janairun 2023, har sai gwamnan bankin Godwin Emefiele ya bayyana a gabanta.
Sai dai Mista Emefiele bai amsa gayyatar ba yana mai cewa ya fita ƙasar waje don a duba lafiyarsa.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
