Connect with us

News

Mabiyan Abduljabbar Kabara zasu kalubalanci hukuncin kisa da aka yanke masa

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Mabiyan malamin nan na Kano Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara a karkashin inuwar Ashabul Kahfi Warraqeem reshen jihar Bauchi sun yanke shawarar daukaka kara kan hukuncin da wata kotun shari’ar Musulunci ta Kano ta yanke na hukuncin kisa ga malamin.

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Da yake zantawa da manema labarai a Bauchi, jami’in hulda da jama’a na kungiyar, Abdullahi Musa, ya yi zargin cewa a siyasance ne gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya aiwatar da hukuncin, inda ya kara da cewa Shehin Malamin na adawa da salon mulkin Ganduje.

Advertisement

Uwa Ta Aurar Da ’Ya Ba Tare Da Sanin Mahaifinta Ba A Kano

 

Musa ya ce, “Ba mu gamsu da hukuncin da aka yanke ba, domin mun yi imanin cewa Gwamnan Jihar Kano Ganduje ne ya yi tasiri a kan lamarin da wasu malamai a jihar wadanda aka san bas aga maciji da shi tsawon lokaci.

Advertisement

 

A cewar Abdullahi Musa gwamnatin Kano ta yiwa shehin malamin kage domin bata masa suna tare da kawar da shi ta hanyar amfani da bangaren shari’a.

Advertisement

 

“Batun hukuncin Shehin Malamin ba komai ba ne illa manakisar bata suna da masu zaginsa da suka shirya ciki kuwa har da Ganduje da wasu malaman addini da ke ganin barazana ga karuwar farin jinin Abduljabbar. Don haka, sun yi ikirarin zargin aikata sabo don ba shi mummunan suna kuma suna da hujjar mugun shirinsu na halaka rayuwarsa,” in Musa.

Advertisement

 

Ya kara da cewa, “Mun yanke shawarar daukaka kara kan hukuncin da aka yanke a wata babbar kotun shari’a domin soke wannan hukunci da bai gamsar da mu ba tare da kwato masa hakkinsa musamman na ‘yancin yin addini da tunani kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.

Advertisement

 

“Muna kira ga Hukumar Kare Hakkin Dan Adam ta Najeriya, Amnesty International, Kungiyoyin kare hakkin bil’adama na kasa da kasa da kuma Lauyoyin kare hakkin bil’adama kamar fitaccen lauyan nan Mista Femi Falana, da mai rajin kare hakkin bil’adama Ahmad Isa, Shugaban kasa, da sauran su da su shiga wannan al’amari.”

Advertisement

 

Yace wannan tsantsar rashin adalci ne da suka yi wa Sheikh Abduljabbar domin kawar da shi daga doron kasa.

Advertisement

 

Musa ya yi zargin cewa gwamnatin jihar Kano da wasu malamai na adawa da Abduljabbar tare da hada kai wajen shirya masa manakisa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending