Connect with us

News

Obasanjo Ya Zama Tamkar Ɗan Baƙin Ciki A Cewar Fadar Shugaban Kasa

Published

on

Fadar shugaban kasa ta mayar da martanin kan kalaman Obasanjo na zabar gwanin,sa
Advertisements
WhatsApp Image 2026 10 20 at 1.48.05 PM

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Fadar Shugaban Kasa ta mayar da kakkausan martani kan kalaman da Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya yi a saƙonsa na sabuwar shekara.

 

Gobara: An Yi Asarar Rayuka 166 A Kano A Shekarar 2022

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa Malam Garba Shehu ya fitar, sanarwar ta ce Obasanjo ba zai taɓa daina caccakar Shugaba Muhammadu Buhari ba sakamakon Obasanjon ba zai daina baƙin ciki kan duk wani wanda ya sha gabansa a ayyukan ci gaban ƙasa ba.

Advertisement

 

Fadar shugaban ƙasar ta buga misali da cewa Shugaba Buhari ya kammala gadar Neja ta biyu bayan an yi shekara 30 ana alƙawura a kanta.

Haka kuma fadar shugaban ƙasa ta ce Obasanjo ya yi wa kudu maso gabashin Najeriya ƙarya domin ya samu ƙuri’unsu, amma Shugaba Buhari bai samu ƙuri’unsu ba amma duk da haka sai da ya yi musu aikin gadar.

Fadar shugaban ƙasa ta kuma ce Obasanjo yana baƙin ciki ne sakamakon yana ganin yadda Buhari ke samun lambobin yabo da kuma yadda shugaban ke ci gaba da da’awar cewa zai tabbatar an gudanar da sahihin zaɓe fiye da wanda ya kawo sa kan karagar mulki.

Haka kuma fadar ta zargi Obasanjo da lalata dimokraɗiyya a Najeriya bayan kitsa tsige wasu gwamnoni a ƙasar nan da suka haɗa da Joshua Dariye da Rashidi Ladoja da Peter Obi da Chris Ngige da Ayo Fayose.

Wannan martanin na fadar shugaban kasa na zuwa ne bayan tsohon Shugaban Najeriyar Chief Olusegun Obasanjo ya ce Peter Obi ne zaɓinsa a zaɓen 2023 haka kuma Obasanjon ya caccaki gwamnatin Shugaba Buhari.

Advertisement

Kalaman Obasanjo dai sun yi matuƙar tayar da ƙura a Najeriya inda tuni manyan jam’iyyu suka soma mayar da martani masu sharhi kuma suna tsokaci.

Dakta Abubukar Kari na jami’ar Abuja, kuma mai nazari kan harkokin siyasa a Najeriya ya ce goyon bayan da Obasanjon ke yi wa Mista Obi ba zai yi wani tasiri ga nasarar ɗan takarar ba.

Domin kuwa a cewarsa a tarihin siyasar Najeriya Mista Obasanjo ko rumfar zaɓensa bai taɓa kawowa ba.

Dakta Kari ya ce “Obasanjo dai tsohon shugaban kasa ne wanda ya mulki Najeriya har sau biyu, kuma ana iya cewa yana da karfin fada-a-ji a ciki da wajen kasar nan – ta bangare daya ke nan – to amma idan ana zaton goyon bayan da ya ba Peter Obi na iya zama hanyar samun yawan kuri’u, ana iya cewa ba shi da tasiri sosai.”

Sai dai yana ganin babban tasirin goyon bayan shi ne, “zai karfafa wa magoya bayan Peter Obi gwiwa, sai dai wasu na ganin yana da tasiri a tsakanin kasashen waje a diflomasiyance, wanda Peter Obin zai iya cin gajiyar haka.”

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending