News
Hukumar Kidayar Jama’a Ta Kasa (NPC) Ta Tsayar Da Ranar Kidayar Jama’a A Najeriya
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Hukumar Kidayar Jama’a ta Kasa NPC, ta ayyana 29 ga watan Maris mai zuwa a matsayin ranar gudanar da aikin kidayar daukacin jama’a da kuma gidajen da ke fadin kasar.
Shugaban NPC, Nasir Kwarra ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Fadar Gwamnatin Tarayya da ke birnin Abuja jim kadan da kammala ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari a wannan Juma’ar.
Wata yar aiki ta gurfana a gaban kotu bisa laifin kashe wata ‘yar shekara 9
A cewarsa, nan da 29 na waran Maris zuwa ranar 2 ga watan Afrilu, ma’aikatanmu za su tsinci kansu a fagen kidayar jama’a.
Shugaban na NPC ya ce, za su tabbatar da ingantaccen aikin kidiyar, yana mai cewa, za su kidaya hatta wadanda ba ’yan Najeriya ba da ke zaune a kasar.
A halin yanzu, bayanai na cewa, yawan al’ummar Najeriya ya zarta miliyan 200.
