Connect with us

News

Gwamnatin Kano Ta Tabbatar Da Bullar Cutar Diphtheria A Kananan Hukumomi 13.

Published

on

DAGA HASSAN KHALID HAMZA 

 

 

 

Gwamnatin jihar Kano ta tabbatar da bullar cutar diphtheria a kananan hukumomi 13 na jihar.

 

Advertisement

Wannan na zuwa ne sa’o’i 48 bayan rahoton da SOLACEBASE ta bayar a ranar Alhamis, inda ya bayyana bullar cutar da ta yi sanadiyar mutuwar mutane 25 kamar yadda ya faru a ranar Juma’ar da ta gabata.

ƘAUYE MAFI DOGON SUNA A DUNIYA

Kwamishinan lafiya na jihar Dr Aminu Tsanyawa ne ya bayyana haka a wani taron tattaunawa kan bullar cutar zazzabin Diphtheria da Lassa a jihar a ranar Asabar.

 

 

 

Ya ce an samu mutane 100 da ake zargin sun kamu da cutar inda uku suka mutu.

Advertisement

 

 

 

 

“Ya zuwa ranar 20 ga watan Janairun 2023 mun sami rahoton bullar cutar guda 100 da ake zargi daga kananan hukumomi 13.

 

Advertisement

 

Su ne kmar haka ”Ungogo, Nassarawa, Bichi, Dala, Dawakin Tofa, Dawakin Kudu, Fagge, Gwale, Kano Municipal, Kumbotso, Kiru, Rano, and Gwarzo.

 

“A cikin mutane 100 da ake zargin an tabbatar da takwas, yayin da muke jiran karin sakamako.

 

 

Advertisement

“Mun rasa rayuka uku daga cikin takwas da aka tabbatar.”

 

 

Tsanyawa ya ce a halin yanzu majiyyata 27 suna karbar magani yayin da 41 kuma aka sallame su.

 

 

Advertisement

 

Kwamishinan ya kara da cewa, a ranar 10 ga watan Janairu, cibiyar bayar da agajin gaggawa ta kiwon lafiyar jama’a ta samu rahoton da ake zargin an kamu da cutar zazzabin Lassa daga asibitin koyarwa na Muhammad Abdullahi Wase da ke Kano.

 

Ya ce an tura wata tawaga domin gudanar da bincike, an dauki samfurin gwajin dakin gwaje-gwaje sannan bayan kwana uku sakamakon ya kamu da zazzabin Lassa.

 

“An dauki samfura 10 daga cikin wadanda ke da hadarin kamuwa da cutar, 3 sun kamu da cutar, jimilla 4 wadanda ke kula da su a asibitin koyarwa na Aminu Kano,” in ji Tsanyawa.

Advertisement

 

Kwamishinan ya ci gaba da cewa gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da cibiyar killace masu cutar ta Kwanar Dawaki domin killace masu cutar zazzabin Lassa.

 

Ya kara da cewa an horar da ma’aikatan lafiya tare da kai su cibiyar keɓewa inda aka ba da shawarar magunguna da kayan masarufi kuma suna da cikakken aiki.

 

Ya kuma yi nuni da cewa jihar za ta gudanar da aikin rigakafi na yau da kullun ga kananan hukumomin da abin ya shafa.(NAN)

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending