Connect with us

Politics

Idan Na Fadi Zaben 2023 Zan Rungumi Kaddara – Kwankwaso

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

 

Advertisement

 

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce zai amince da sakamakon zaben shugaban kasa na 2023 idan har bai samu nasarar lashe shi ba.

Advertisement

 

Kwankwaso ya bayyana hakan ne ranar Litinin a wani taro da ya yi da ma’aikata da daliban Jami’ar Abuja.

Advertisement

Mutum 4 Sun Shiga Hannu Kan Zargin Satar Jaririya A Zamfara

 

Aminiya ta rawaito cewa, Sai dai ya ce akwai bukatar a gudanar da zaben cikin gaskiya da adalci.

Advertisement

 

Tsohon Gwamnan na Jihar Kano ya kuma ce, “Ba ni da matsala da amincewa da faduwa zabe. Hanya mafi kyau ta yarda da zaben 2023, ita ce ta hanyar yin abin da ya dace – wato yin zabe na gaskiya, zaben da kowa zai aminta da shi,” in ji shi.

Advertisement

 

Kwankwaso, wanda kuma tsohon Ministan Tsaro ne, ya yi alkawarin kara wa sojojin kasar nan karfi, a wani yunkuri na sabunta dabarun tsaro.

Advertisement

 

A yayin taron Kwankwaso, ya jaddada wa dalibai da ma’aikatan Jami’ar kudurinsa na farfado da harkar ilimi a kasar nan, inda ya bayyana irin tanadin da ya yi wa harkar.

Advertisement

 

“Mun yanke shawara kuma muna nan kan tsarinmu cewa za mu magance matsalar rashin tsaro.

Advertisement

 

“Za mu ba da dama mai yawa ga matasa maza da mata su yi wa kasar nan hidima a matsayin jami’an soja, ’yan sanda, jami’an DSS da sauransu.”

Advertisement

 

Game da batun yiwuwar janye wa wani takararsa kuwa, Kwankwaso ya ce bakin alkalami ya riga ya bushe.

Advertisement

 

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending