Connect with us

News

An gurfanar da wani maigadi a kotu kan zargin satar bulo

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

 

An gurfanar da wani maigadi a kotu kan zargin satar bulo 240 a yankin Abuja.

 

A ranar Litinin ’yan sanda suka maka mai gadin a kotun da ke yankin Kado inda ake tuhumarsa da laifin hadin baki da sata.

Advertisement

 

Sean Dyche Ya Zama Sabon Kocin Everton

Lauyan mai gabatar da kara, Stanley Nwafoaku, ya fada wa kotun cewa a ranar 7 ga Janairu suka mika korafin satar a ofishin ‘yan sanda da ke Life Camp.

 

Amininiya ta rawaito cewa Ya ce ya dauki mai kare kansa aiki don tsare masa kamfanin buga bulo dinsa.

 

 

Advertisement

Ya yi zargin mai gadin ya hada baki wani wajen sace masa bulo har guda 240 wanda kudinsu ya kai N15, 000.

 

Laifin da lauyan ya ce ya saba wa sassa na 79 da 289 na dokar ‘Penal Code’.

 

Shi kuwa lauyan wanda ake zargi, Charity Nwosu, nema ya yi kotun ta ba da belin wanda yake karewa.

 

Advertisement

Alkalin kotun, Muhammed Wakili, ya ba da belin wanda ake zargi kan N200,000 da shaida daya, kana ya dage shari’ar zuwa 1 ga Maris.

 

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending