Entertainment
Kotu ta aike da Murja Kunya zuwa gidan yari
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kotun shari’ar Muslunci da ke Filin Hoki a Kano ƙarƙashin mai Shari’a Abdullahi Halliru ta aike da Ƴar TikTok ɗin nan Murja Ibrahim Kunya zuwa gidan yari.
Lauya Barrister Lamiɗo Abba Soron Ɗinki ya karanto mata ƙunshin tuhume-tuhumen da ake mata wanda ta musanta.
Ana zargin Murja da ɓata suna da barazana ga Aisha Najamu ta Izzar So da kuma Ashiru Idris wanda dukanninsu abokananta ne.
Kotun ta ɗage sauraron ƙarar zuwa 16 ga watan Fabrairun da muke ciki.
Sai dai Lauyan Murja Barrister Yasir Musa ya nemi a tura ta zuwa Hisbah maimakon gidan Yari sai dai Kotun bata amince ba.
-
News6 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News4 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News6 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
