News
Masifar girgizar ƙasar Turkiyya ta haifar da wasu musifu
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
An samu nasarar kashe wutar da ta tashi a ɗaya daga cikin manyan tashoshin ruwan Turkiyya, kamar yadda Ma’aikatar Tsaro ta ƙasar ta bayyana.
Girgizar ƙasar da aka fuskanta a Turkiyya ranar Litinin ce ta haifar da gobarar a garin Iskenderun da ke gabar Bahar Rum.
Dubban tantuna ne suka kama da wuta kuma hayaƙin wutar ya baibaye ko ina a cikin gine-gine.
Duk da cewa an kashe wutar, amma wakilin BBC ya ce hayaki har yanzu yana fitowa daga inda wutar ta tashi.
Ma’aikatar tsaro ta ce ana amfani da jiragen sama da na sojoji domin kashe wutar.
An dakatar da duka ayyukan tashar jirgin ƙasar baki ɗaya.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
