An baza jami’an ƴan sanda a sassan birnin Lagos na Najeriya domin dakile tarzomar da ta ɓarke wadda ake kyautata zaton tana da nasaba da matsalar ƙarancin takardun kudin ƙasar na naira da ake fuskanta.
Rahotanin sun ce wasu manyan bankunan kasuwanci da ke birnin sun ci gaba da kasancewa a rufe.
DA DUMI-DUMI: CBN ya umurci bankunan da su karbi tsofaffin takardun kudi na N500, N1,000
An riƙa jin ƙarar harbe-harben bindiga kuma an toshe manyan hanyoyi da dama inda wasu suka yi amfani da tayoyin da ke ci da wuta.
Ƴan sanda sun ce an dawo da doka da oda a gundumar Mile 12, sannan sun ɗora alhakin tashin hankalin a kan ɓata-gari.
Jama’a na fushi a kan ƙarancin sababbin takardun kuɗin da aka sauya wa fasali, abin da ya haifar da zanga-zanga a farkon makon da ake ciki.
Gwamnan jihar Babajide Sanwo-Olu ya fito ya roƙi al’umma da su guji yin zanga-zanga a kan canjin kuɗin.
Ya ce gwamnati na yin duk abin da ya kamata domin rage wahalhalun da jama’a ke sha a kan ƙin karɓar tsofaffin kuɗin da kuma ƙarancin man fetur.
