News
Bayan Ƙorafin da NNPP tayi An Sauyawa Kwamishinan Yan Sandan jahar Kano Wurin Aiki
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Jim kadan bayan jam’iyyar NNPP ta nemi a cire kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Mamman Dauda bisa zargin nuna bangaranci babban Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, Alkali Usman Baba ya sauya masa wurin aiki zuwa jihar Plateau.
A jiya Lahadi ne dai jam’iyyar NNPP tayi barazanar gudanar da zanga zanga a kananan hukumomi 44 bisa yadda tace Kwamishinan Yan Sandan yana nunawa mambobinta.a tsakanin jam,iyya Mai Mulki da mara Mulki banbanci
Sai dai cikin wata takarda da jaridar DAILY NIGERIAN ta samo ta nuna cewa an tura Mamman Dauda zuwa jihar Plateau yayin da aka turo Muhammad Yakubu zuwa Kano.
-
News5 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News7 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News6 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
