Connect with us

News

Yan sanda sun kama ‘yan bangar siyasa 85 a Kano

Published

on

 

 

Advertisement

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce ta kama mutane 85 waɗanda ta ke zargin ‘yan bangar siyasa ne tare kuma da ƙwato muggan makamai.

 

Advertisement

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar , SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ta ce suna ci gaba da binciken mutanen da suka kama.

Zaɓen 2023: Za a rufe iyakokin Najeriya na sa’a 24

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, ya gode wa al’umma jihar bisa haɗin-kai da suke bai wa rundunar, inda ya roki goyon bayansu wajen ganin an gudanar da zaɓe mai gaskiya a Najeriya.

Advertisement

 

A jiya ne dai aka samu rikici lokacin da magoya bayan jam’iyyar NNPP suka je tarbar ɗan takarar shugaban ƙasar na jam’iyyar, Injiniya Rabi’u Musa kwankwaso a jihar Kano lamarin da ya janyo jikkatar mutane da dama tare da ƙona motoci.

Advertisement

 

Jam’iyyar NNPP na zargin ‘yan jam’iyyar APC da kai musu harin a yayin da ‘yan APCn kuma suka musanta.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending