News
Pakistan ta haramta yaɗa jawaban tsohon firaministan ƙasar a kafofin yaɗa labarai
Hukumar kula da kafofin yaɗa labarai ta Pakistan ta haramta wa gidajen talbijin yaɗa jawabai da hirarrakin tsohon firaministan ƙasar Imran Khan.
Cikin wata sanarwa da PEMRA ta fitar, ta ce mista Khan ya sha yin zarge-zarge marasa tushe kan hukumomin ƙasar da kuma yaɗa kalaman ƙiyayya.
Yan sanda sun kashe mutum biyu da ake zargi da garkuwa da mutane a Bauchi
Bbc ta rawaito cewa Lamarin na faruwa ne yayin da Khan ɗin ya zargi gwamnati da kai shi Kotu kan tuhume-tuhume marasa tushe.
Dubban magoya bayansa sun taru a kofar gidansa don daƙile yunƙurin ‘yan sanda na kama shi kan zargin bayyana kyautukan da ya samu daga ƙasashen waje a lokacin da yake kan mulki.
Advertisements
