Connect with us

News

NBC ta haramta sanya batutuwan addini da na ƙabilanci a shirye-shiryen siyasa

Published

on

Hukumar kula da kafofin yaɗa labarai ta kasa  ta ce ta lura da yadda ake sanya abubuwan da suka shafi addini da ƙabilanci da kuma kalaman tunzura jama’a a shirye-shiryen siyasa da yaƙin neman zaɓe a yayin da ake fuskantar zaɓen gwamnoni a ƙasar.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce yin hakan ba zai zame wa ƙasar alkairi ba.

Advertisement

Bankuna Sun Fara Mayar Wa ‘Yan Najeriya Tsoffin Takardun Naira.

Hukumar ta ce doka ta tanadar da cewa dole kafofin yaɗa labarai su taimaka wajen jaddada hadin kan ƙasa tare da taimaka wa wajen inganta dimokradiyya.

Haka kuma sanarwar ta yi kira ga kafofin yaɗa labaran ƙasar da su yi amfani da kafofin nasu wajen daƙile wannan aƙida, da kuma kalaman tunzura jama’a da za su iya kawo barazana ga haɗin kai da dimokraɗiyyar ƙasar.

Advertisement

A cewar sanawar duk da cewa ana ƙarfafa wa kafofin yaɗa labarai gwiwwa wajen bai wa ‘yan ƙasa damar bayyana ra’ayoyinsu, waɗanda ba kalaman ƙiyayya ko na cin zarafin juna ko na tunzura jama’a ba, ya kamata kafofin yaɗa labaran su san cewa za su yi hakan ne kawai ta hanyar da ta dace.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending