Connect with us

News

Bankuna Sun Fara Mayar Wa ‘Yan Najeriya Tsoffin Takardun Naira.

Published

on

 

 

Advertisement

 

Biyo bayan hukuncin da kotun kolin Najeriya ta yanke, wanda ya kara wa’adin dokar amfani da tsohon kudin kasar nan zuwa watan Disamba, wasu bankunan ajiya sun fara biya da tsoffin takardun kudi.

Advertisement

Binciken da jaridar Daily Trust ta gudanar, ya nuna cewa wasu bankunan kasuwanci a birnin Kano da Abuja sun fara bawa jama’a tsofaffin takardun kudi na Naira 500 da kuma 1000.

Kotu Ya Ba da Belin Hon. Ado Doguwa

Yayin da wasu rassan bankin Guarantee Trust Bank (GTB) suka fitar da tsoffin takardun kudin, wasu kuma kamar bankin Polaris da ke Abuja ba su fara ba har yanzu.

Advertisement

Majiyoyi daga bankin GT sun ce sun sami umarni daga hukumominsu kan su fara bawa jama’a tsoffin takardun kudi.

Masana harkokin tattalin arziki sun bukaci shugaban kasar Muhammadu Buhari da ya umurci gwamnan babban bankin CBN, Godwin Emefiele, da ya yi biyayya ga hukuncin da aka yanke kan ci gaba da amfani da tsoffin takardun kudin har zuwa watan Disambar.

Advertisement

Har yanzu dai al’amuran kasuwanci da dama sun daina gudana yadda ya kamata, sakamakon karancin takardun kudin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending