Business
Yadda Bankuna Suka Koka Kan Samun Karancin Takardun Kudi A Jihar Kano
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Bankunan kasuwanci a jahar Kano sun bayyana damuwarsu akan yadda babban bankin kasa CBN ya takaita ba su takardun kudi na Naira, inda suka bayyana cewa da yuwuwar a samu karancin takardun Kudi.
Wakilin jaridar Inda Ranka ya ziyarci bankuna da dama da suka hadar da Bankin Zenith da bankin GTa Kasuwar singa inda dukannin su suka bayyana damuwa akan al’amarin.
Wasu Batagari Sun Yi Yunkurin Kubutar Da Masu Laifi A Ofishin Yan Sanda A Kano
A sakamakon karancin samun takardun kudi, wasu bankuna sun rage adadin kudin da suke bari a cire a cikin bankin.
Sai dai wani ma’aikaci a daya daga cikin bankunan daya bukaci a sakaya sunan sa, yace abunda yake tunanin ka iya kawo wannan matsalar shine Mutane sun rage kawo ajiyar kudi a bankunan.
A yayin da bankunan suke fama da wadanan matsaloli, babu wani bayani akan dalilin takaita samar da takardun kudin ga bankuna daga bangaren babban bankin kasa wato CBN.
A wani labarin kuma Wasu Batagari Sun Yi Yunkurin Kubutar Da Masu Laifi A Ofishin Yan Sanda A Kano
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
