News
Dage zaben gwamnoni yasa za’a dage Kidayar jama’a
Fara kidayar gidaje da yawan jama’a na kasa na shekarar 2023, wanda tun farko aka shirya yi a ranar 29 ga Maris, dage zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi na iya shafan kidayar jama’a.
Shugaban hukumar kula da yawan jama’a na kasa Nasir Kwarra ne ya bayyana hakan a lokacin da yake jawabi a wajen wani taro da wakilin gidauniyar kula da yawan al’umma ta Majalisar Dinkin Duniya a Abuja.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta tsara gudanar da zabukan jihohin da tun farko a ranar 11 ga watan Maris.
Duk da cewa babu takamaiman ranar da za a fara atisayen, Kwarra ya shaida wa manema labarai cewa zai tuntubi shugaban kasa Muhammadu Buhari domin ranar da ta dace da kidayar jama’a.
Channel
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
