Connect with us

News

Ƴan sanda sun rufe majalisar dokokin jihar Filato kan rikicin shugabanci

Published

on

Rundunar ƴan sandan jihar Filato ta rufe zauren majalisar dokokin jihar kan rikicin shugabanci da ake ci gaba da yi.

Jami’an kwantar da tarzoma sun isa harabar majalisar ne da misalin karfe 5 na safiya, inda suka toshe hanyar shiga majalisar.

Advertisement

Bai Kamata ba Gwamnatin Tarayya Ta Fara Tunanin Cire Tallafin Man Fetur A Yanzu Ba – Dr Abdulrazak Fagge

Duk da cewa babu wata sanarwa a hukumance daga rundunar kawo yanzu, amma rahotanni na bayyana cewa hakan ba ya rasa nasaba da rikici tsakanin mambobin majalisar kan wanda zai shugabanceta.

Kawunan ƴan majalisar ya rabu gida biyu, inda wasu ke ɓangaren kakakin majalisar na yanzu Rt. Hon Yakubu Sanda yayin da wasu kuma ke goyon bayan kakakin majalisar da aka mayar kan kujerar Rt. Hon Ayuba Abok wanda aka tuɓe a watan Oktoban 2021.

Advertisement

Wata kotu ce ta sake mayar da Abon kan kujerarsa ta shugaban majalisar a ranar Litinin, inda washegari ya yi bayyana a majalisar a matsayin shugaba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending