Connect with us

News

Yadda direban jirgin sama ya yi artabu da maciji a sararin samaniya.

Published

on

 

An yaba wa wani matuƙin jirgin ɗan Afirka ta Kudu kan nasarar saukar gaggawa da ya yi, bayan da ya lura da wani maciji nau’in gamsheƙa a ƙarƙashin kujerar zamansa.

 

Rudolph Erasmus ya ɗauko fasinjoji huɗu daga birnin Cape Town zuwa arewacin Nelspruit da safiyar ranar Litinin amma saboda artabun da ya yi da gamsheƙar ya sa shi saukar gaggawa, kamar yadda kafofin yaɗa labaran ƙasar suka ruwaito

Matar gwamnan Kano na farko, Hajiya Ladi Audu Bako, ta rasu

Direban ya shaida wa kafar yaɗa labarai ta Time Live cewa “ina duba ƙarƙashin kujerata, kawai sai na ga macijin na ƙoƙarin mayar da kansa ƙarƙashin kujerar”.

 

Advertisement

Sarar gamsheka zai iya kashe mutum cikin mintuna 30 idan ba a ɗauki matakan da suka dace ba.

 

Minista harkokin sufurin jiragen sama ta Afirka ta kudu ya yaba da jarumtar Mr Eramus, kamar yadda shafin yanar gizo na news24 ya ruwaito.

 

Direban jirgin yace ya shiga yanayi mai rikitarwa wajen fada wa fasinjojin ainihin abin da ya sa ya yi saukar gaggawar.

 

Advertisement

“Na fada musu cewa akwai matsala., akwai maciji a cikin jirgin. Ina da yaƙinin cewa yana ƙarƙashin kujera ta don haka za mu yi saukar gaggawa”.

 

Ya yi ƙoƙarin ganin ya yi saukar gaggawa a birnin Welkom dake Afirka da Kudu.

 

Injiniyoyin da suka caje jirgin ba su ga gamsheƙar ba, inji Mr Eramus.

 

Advertisement

Ya ce yana sa ran komawa bakin aikinsa a ranar Laraba.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending