News
Zelensky na ziyara a Poland karon farko tun bayan mamayar Ukraine
A karon farko tun bayan mamayar Rasha, shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky, zai kai ziyara Poland.
Poland na ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi magana da kuma bayar da cikakken goyon baya ga Ukraine tun da aka fara yaki.
Dan Jaridar Da Aka Kora Saboda Caccakar Gwamnan Borno Ya Sami Aiki A Turkiyya
Ta karɓi bakuncin miliyoyin ‘yan gudun hijira daga Ukraine, sannan ta aike mata da tankunan yaki fiye da 300.
Kazalika ita ce ƙasar farko davta aike wa Ukraine jiragen yaki.
Ana kyautata tsammanin Mr Zelensky zai gode wa al’ummar ƙasar a fadar ƙasar da ke Warsaw.
Amma kuma zai yi bayani a kan yankunan da har yanzu ake zaman ɗar-ɗar a ƙasarsa.
Manoman Poland sun nuna fushinsu a kan yadda ake shigar da hatsin Ukraine cikin kasarsu inda suka ce yana karya farashin nasu
