Connect with us

News

Majalisa: Kudirin haramtawa likitocin Najeriya aiki a waje

Published

on

Wani kudirin doka da zai hana likitocin Najeriya ficewa daga kasar har sai sun yi aikin tsawon shekaru 5 a cikin gida, ya tsallake karatu na biyu a majalisar wakilai.

 

Manufar dokar itace dakile karuwar adadin likitocin dake ficewa aiki waje, bisa kwadaituwa da kyakkyawan yanayi.

Advertisement

 

Mamba a majalisar, Ganiyu Abiodun Johnson ne ya dauki nauyin kudirin, wanda aka yi wa take da ‘kudirin yiwa dokar likitoci ta 2004 kwaskwarima’.

Advertisement

NAHCO ta fitar da kudin aikin Hajjin bana ga jahohin yankin Arewa.

Johnson yace zai fi kyautuwa likitocin su fara amfanar da cikin gida da kwarewar da suka samu karkashin kulawar kasa, akalla da shekaru 5 kafin su fice.

 

Advertisement

Zaman majalisar na ranar Alhamis, 6 ga watan Aprilu, karkashin jagorancin Femi Gbajabiamila ya amince da wannan kudiri a karatu na biyu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending