News
NAHCO ta fitar da kudin aikin Hajjin bana ga jahohin yankin Arewa.
Hukumomin kula da sha’anin maniyyata aikin hajji a bana sun fitar da wasu alkaluman bayanai game da aikin Hajjin na bana.
Bayanan sun shelanta cewar farashin Kudin aikin Hajjin Bana a jihar Kaduna da sauran jihohin arewacin Najeriya ya Kai Naira Miliyan Biyu, da Dubu Dari Tara da Sha Tara (2,919,000).
Jihar Kaduna ta kasance jihar data fi ko wace jiha samun yawan kujerun maniyyatan a bana.
Rahotan hakan na kunshe cikin wata wallafa da maitemakawa sakataren hukumar Ibrahim Shehu Giwa ya wallafa a shafin sa.
Ibrahim, yace ana son maniyyata su kammala biyan kudin su daga nan zuwa sati 2, wato 21st April 2023, inda ake fatan Jirgin farko zai tashi zuwa kasa me tsarki ranan Lahadi, 21st May 2023.
Kafin yanzu farashin kujerar aikin Hajjin bai taba kaiwa wannan farashin ba, sai dai masu bibiyar Shaanin sun alakanta hakan da farashin Mai da kuma tsadar dakunan Otel a kasa mai tsarki, da sauran tsare-tsare.
