Connect with us

Sports

Haaland ya ci kwallo ta 45 yayin da Man City ta lallasa Bayern

Published

on

Erling Haaland ya ci kwallonsa ta 45 a kakar wasa ta bana bayan da Manchester City ta doke Bayern Munich da ci 3-0 a zagayen farko na wasan daf da na kusa da na karshe na gasar cin kofin zakarun Turai ranar Talata, inda ta haye wasan kusa da na karshe.

Rodri da Bernardo Silva na cikin wadanda suka taimakawa zakarun na Ingila, dake hubbasa don lashe babbar gasar a karon farko.

Advertisement

Mutum 12 Sun Rasu A Hatsarin Mota A Ebonyi

Mintuna 27 da fara wasa City ta ci kwallon ta hannun Rodrigo Hernandez, shi kuwa Bernardo Silva ya kara ta biyu bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, sai kuma Erling Haaland ya ci na uku bayan mintuna bakwai.

Wasa na bakwai kenan suka kara tsakaninsu a Champions League, kuma City ta ci hudu, Bayern ta yi nasara a uku.

Advertisement

Inter Milan

Inter Milan ma ta kai matakin wasan dab da na karshe a gasar cin kofin zakarun Turai bayan doke Benfica da ci 2 – 0 bayan da Nicolo Barella da Romelu Lukaku suka ci kwallo guda-guda a Lisbon.

Advertisement

Milan ta ci kwallon farko ta hannun Nicolo Barella, bayan da suka koma karawar zagaye na biyu.

Romelu Lukaku, wanda ke wasa amtsayin aro daga Chelsea shine ya zura na biyu a raga a bugun fenariti, saura minti takwas a tashi wasa.

Advertisement

Karo na hudu da suka kece raini a tsakaninsu, inda Inter ta ci uku da canjaras daya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending