News
Mene ne bambancin yin Umrah cikin azumi da sauran lokuta
Umrah kalma ce ta Larabci wadda ke nufin ziyara, kamar yadda Dakta Abubakar Sani Birnin Kudu, babban limamin Dutse da ke jihar Jigawa ya bayyana.
Malamin ya ce a shari’ance Umrah na nufin ziyarar ɗakin Allah (Ka’aba) da nufin yin ibada, wadda ta ƙunshi shiga halin Ihrami da Talbiya da Ɗawafi da Sa’ayi tsakanin Safa da Marwa da kuma aski.
Yin Umrah na ɗaya daga cikin ibadu mafiya tarin lada da al’ummar Musulmai ke yi domin samun gwaggwaɓan ladan da ke tattare da yinsa.
Matsayin Umara a addinin Musulunci
Dakta Abubakar Sani Birnin Kudu ya ce malaman duniya sun haɗu a kan ra’ayi ɗaya cewa umara abu da da aka shar’anta yinsa.
”Ma’ana abu ne da ya zo a shari’ance ana dalilin a ayi shi”
Sai dai malamin ya ce dangane da matsayinsa a shari’a an samu saɓanin malamai inda wasu ke ganin mustahabbi ne, kamar Imamu Malik da Abu Hanifa.
Sai kuma ra’ayin Imamu Ahmad bin Hambal da Imamu Shafi’i waɗanda suke ganin wajibi ne yin umara amma sau ɗaya a rayuwar mutum, ba kowacce shekara ba.
”Lallai Umrah tana cikin ibadu masu muhimmanci, don haka yana da kyau mutum ya samu ya yi a ko da sau ɗaya ne a rayuwarsa” in ji Malamin.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
