Connect with us

News

Ma’aikatan NPC Sun Gudanar Zanga-Zanga Kan Wani Zargi Da Suke Yi A Kano

Published

on

 

 

Advertisement

 

Sama da ma’aikatan wucin gadi 300 na Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC) a Kano sun gudanar da zanga-zanga kan rashin biyansu alawus-alawus na horon kwanaki 18 tun daga watan Fabrairun 2023.

Advertisement

 

Jaridar indaranka ta tattaro cewa Mai magana da yawun su Aliyu Rulwanu ya zargi hukumar da tsarin biyan kudi wanda a cewarsa ya sabawa ka’idojin da aka cimma.

Advertisement

 

Bangarorin Sudan ba su da niyyar kawo karshen rikicin nan kusa – MDD

“A lokuta da dama mun sha rubuta wasiku na koke ga dukkan hukumomin da abin ya shafa kan halin da ma’aikatan wucin gadi ke ciki dangane da rashin biyan su alawus da ba a yi ba duk da cewa mun samu mu tabbacin za an biya su. Ba mu da wani zabi da ya wuce mu shiga wannan zanga-zanga ta lumana,” inji shi.

Advertisement

 

Jaridar Daily trust ta rawaito cewa Da aka tuntubi jami’ar hulda da jama’a ta NPC reshen jihar Kano, Jamila Abdulkadir Sulaiman, ta bayyana cewa ma’aikatan sun tafka kura-kurai wajen cike fom din kuma hukumar na daukar lokaci domin gyara su.

Advertisement

 

“Sun yi ikirari cewa wasu daga cikinsu sun karbi dukkan kudadensu kuma hakan ya faru ne saboda sun cika fom dinsu daidai. Ina so in sake kira gare su da su kara hakuri domin nan ba da dadewa ba kowa zai samu kudinsa,” inji ta.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending