Connect with us

News

An Nada Sabon Kwamishinan ’Yan Sandan Kano Da Wasu guda sha daya

Published

on

Hukumar Aikin Dan Sanda ta nada sabon kwamishinan ’yan sandan jihohin Kano da Kaduna da wasu jihohi 10.

 

Advertisement

Hukumar ta yi sauyin ne a shirye-shiryenta na tabbatar da tsaro gabanin ranstar da sabuwar gwamnati da ke tafe ranar 29 ga watan Mayu mai kamawa.

Ma’aikatan NPC Sun Gudanar Zanga-Zanga Kan Wani Zargi Da Suke Yi A Kano

 

Advertisement

Hakan kuwa na zuwa ne makonni kadan bayan karin girma da kwashinonin ’yan sandan jihohin suka samu karin girma zuwa matsayin Mataimakin Sufeto-Janar.

 

Advertisement

A kan haka ne ta turo Mohammed Usaini Gumel a matsayin sabon Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Kano.

 

Advertisement

Sauran jihohin da aka tura wa sabbin Kwamishinonin ’Yan Sanda su ne:

 

Advertisement

ABUJA: Haruna Gabriel Garba.

KADUNA: Garba Musa Yusuf.

Advertisement

ZAMFARA: Garba Ahmed.

SAKKWATO: Hayatu Kaigama Ali.

Advertisement

KATSINA: Aliyu Musa.

YOBE: Mohammed Nuni.

Advertisement

BINUWAI: Julius A. Okoro.

DELTA: Tajudeen A. Abass.

Advertisement

OGUN: Oladimeji Yomi Olarewaju.

ONDO: Taiwo Jesubiyi.

Advertisement

BAYELSA: Romokere Ibiani.

Da yake jawabi bayan sanar da nadin sabbin kwamishinonin, shugaban hukumar aikin dan sanda, Solomon Arase, ya bukace su da su kasance masu sadaukarwa a yayin gudanar da aikinsu.

Advertisement

 

Arase, wanda tsohon Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Najeriya ne, ya jaddada cewa aikin ke gaban sabbin kwamishinonin ’yan sandan, musamman a wannan lokaci na sauyin gwamnati yana bukatar kishin kasa da bullo da sabbin dabaru da kuma jajircewa.

Advertisement

 

Don haka ya umarce su da su gaggauta komawa sabbin wuraren aikinsu su shirya wa aikin da ke gabansa.

Advertisement

 

Ya kara da cewa hukumar za ta rika sanya ido a kansu domin tabbatar da ganin cewa, su da jami’ansu ba su yi sakaci ko wuce gona da iri wajen gudanar da aikinsu ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending