News
Mutanen Da Suka Gamu Da Tangardar Na’ura Zasu Sake Rubuta Jarabawar Jamb
Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu ta kasa JAMB zata sake baiwa wadanda suka gamu da kalubale na tangardar na’ura a lokacin rubuta jarabawar UTME a ranar Talata, damar sake rubuta jarabawar.
Mai magana da yawun hukumar, Febian Benjamin ne ya baiyana haka a Abuja jim kadan bayan wani taron gaggawa da jami’an hukumar suka gudanar, inda aka tattauna kan kalubalen da aka fuskanta game da rubuta jarabawar a rana ta farko.
Ma’aikatan NPC Sun Gudanar Zanga-Zanga Kan Wani Zargi Da Suke Yi A Kano
Ya ce kimanin cibiyoyi 100 daga cikin 708 da aka rubuta jarabawar ne suka fuskanci kalubale na tangardar na’ura wanda ya hana mutane rubuta jarabawar.
A saboda haka y ace duk wanda yake da irin wannan matsala zai sake fitar da sabon Slip na rubuta jarabawar a yau,domin sanin lokacin da zai sake zama jarabawar da kuma wuri.
