News
An kashe mutane fiye da 500 a Kudancin Kaduna cikin shekara 6
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Shugaban Ƙungiyar ci gaban al’ummar Atyap a jihar Kaduna, Mista Samuel Achi ya bayyana cewa daga shekarar 2017 zuwa yanzu, an kashe mutum 518 sannan dubbai sun tsere, an kuma ɗaiɗaita ƙauyuka 20 yayin da aka ƙone wasu ƙauyukan 18 a Kudancin Kaduna.
Shugaban ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai da aka gudanar a yau a Samaru Kataf. Ya ce hare-haren da ake ci gaba da kai wa sun yi kamanceceniya da waɗanda aka kai a 2019 kuma wasu ɓatagari ne suke kai wa waɗanda kuma ya kamata a ce hukumomin tsaro sun hukunta su.
Jaridar Punch ta rawaito Mista Achi na “kira ga al’ummarmu da su kare kansu daga duk wasu hare-hare,” in ji shi inda ya ce an kai maƙura.
Da yake kokawa kan zargin da ake cewa sojoji na da hannu, Mista Achi ya ce sojojin da aka tanada domin tabbatar da tsaro a yankin, ba sa yin wani abu na kawo sauƙi.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
