Connect with us

News

Gwamnatin Tinubu ce za ta kaddamar da babbar hanyar Legas zuwa Ibadan—-Fashola

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, ya ce gwamnatin mai jiran gado ta Sanata Bola Tinubu ce za ta kaddamar da babbar hanyar Legas zuwa Ibadan.

Advertisement

Channels tv ta rawaito cewa Fashola ya bayyana hakan a ranar yayin wani taron majalisar zartaswa na kasa da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a zauren majalisar da ke fadar gwamnatin tarayya Abuja.

Ɗaliba ta tayar da gobara a makaranta saboda an ƙwace mata waya.

A cewar ministan, ranar 30 ga watan Yuni ne aka shirya fara kaddamar da muhimman aikin na al’umma.

Advertisement

Ya bayyana cewa, akwai wani bangare mai mahimmanci a cikin aikin mai nisan kilomita hudu zuwa Legas wanda ya kasance abin fasaha ne amma abin da ya jinkir kammala shi, shi ne ma’aikatarsa ​​ta gano wata lakar kasa ce a wurin.

Bayan haka, Fashola ya gayyaci shugaba Buhari da ya kaddamar da wasu ayyuka da ma’aikatar sa ta fara aiwatarwa a fadin kasar nan.

Advertisement

Ayyukan dai Sun hada da sakatariyar gwamnatin tarayya mai suna Dr Goodluck Jonathan da ke Yenagoa na jihar Bayelsa; Sakatariyar Tarayya ta Ebele Okeke da ke Awka na Jihar Anambra; da sakatariyar Malam Yahaya dake Gusau a jihar Zamfara.

Sauran sun hada da gadar Loko-Oweto da ta hada jihohin Nasarawa da Benue, gadar Ikom dake jihar Cross Rivers da dai sauransu

Advertisement

Ministan ya kuma bayyana cewa an sanya wa sabuwar gadar Neja ta biyu sunan shugaba Buhari.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending