Connect with us

News

Ministocin Buhari Sun Fara Mika Ragamar Aiki Gabanin Karewar Wa’adin Mulki

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

Kwanaki biyar gabanin karewar wa’adin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ministoci sun fara mika ragamar aiki ga  manyan sakatarori a ma’aikatunsu gabanin rushe majalisar zartaswa.

A ranar litinin 29 ga watan Mayu na 2023 wa’adin mulkin shugaba Buhari na shekaru 8, wanda ya fara daga ranar 29 ga watan Mayun 2015 zai kare.

Advertisement

Sujjadar Cristiano Ronaldo bayan nasarar zura kwallo ta janyo cece-kuce

Wata majiya ta fadawa manema labarai cewa a yau ne Ministoci zasu ajiye aiki hukumance duk da cewa Shugaba Buhari bai bayyana rusa majalisar ministocin tarayya ba.

Bayanai sunce ministan tsaro, Bashir Magashi, ya umurci babban sakataren ma’aikatar Ibrahim Kana da ya karbi ragamar aiki.

Advertisement

Shima ministan wasanni, Sunday Dare, zai  mika ragama ga  babban sakatare na ma’aikatarsa Alhaji Ismaila Abubakar ayau.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending