News
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf Ya Kwace Asibitin Hasiya Bayero Da Gwamnatin Ganduje Ta Siyar
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Gwamnan jihar Kano Engr Abba Kabir Yusuf ya kwace sanannen asibitin yara ɗaya tilo da ke cikin birnin Kano wanda aka fi sani da Hasiya Bayero.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata ziyarar da kai asibitin jiya lahadi inda ya duba halin da asibitin yake ciki.
yaƙi da Amurka zai zama wani bala’i da ba za a iya jurewa ba a duniya.
Asibitin na Hasiya Bayero wanda ya shafe shekaru 33 yana aiki, asibitin yara ne da yake karbar yara marasa lafiya daga kusan illahirin kananan hukumomin jihar Kano da kuma makotan jihohi.
Engr Abba ya bayar da umarnin a gyara asibitin nan take, a mayar da shi na zamani domin al’umma su ci gaba da amfani da shi.
Gwamnan ya nuna bacin ran sa yadda ana tsaka da amfani da asibitin, gwamnatin tsohon gwamna Ganduje ta siyar da asibitin, ta kuma tashi jama’a marasa lafiya da likitoci.
“Kowa aka ba asibitin Hasiya Bayero mun ƙwace shi, kuma mun dawo wa da talakawa haƙƙin su” a cewar Abba.
Rahotanni sun ce gwamnatin tsohon gwamna Ganduje ta siyar da asibitin akan Naira miliyan 6 kacal.
-
News2 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News2 days ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News3 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
