News
yaƙi da Amurka zai zama wani bala’i da ba za a iya jurewa ba a duniya.
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Ministan tsaron China ya ce yaƙi da Amurka zai zama wani bala’i da ba za a iya jurewa ba ga duniya.
Ya bayyana haka ne a jawabinsa na farko tun bayan da ya hau kan muƙamin.
A wani taron tsaro, Janar Li Shangfu ya ce wasu ƙasashe suna tseren shigar da makamai nahiyar Asiya.
Hukumar NDLEA Ta Kama Mutum 26 Kan Zargin Safarar Kwayoyi A Gombe
Tun farko Amurka ta yi zargin rashin tsaro kan wani jirgin ruwan China da ke watangaririya kusa da wani jirgin ruwan yaƙin Amurka a yankin Taiwan.
A jiya Asabar ne, rundunar sojin ruwan Amurka ta ce wani jirgin ruwan China ya shiga hanyar da ba ta dace ba kusa da wani jirgin ruwan Amurka yayin da yake ratsa mashigin Taiwan tare da jiragen ruwan Canada.
China dai ta soki duka ƙasashen biyu sai dai Amurkar da Canada sun ce suna tafiya ne a inda dokokin ƙasa da ƙasa suka amince da.
Janar Li wanda ya zama ministan tsaro a Maris ya zargi Amurka da tafiya kan zamanin cacar baka abin da ya ce yana barazana sosai ga tsaro.
-
News2 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News2 days ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News3 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
